Kotun ƙararrakin zaɓe ta Jihar Kano ta bayyana Laraba, a matsayin ranar da za ta yanke hukunci kan ƙorafi game da zaɓen gwamnan Kano.
Sojoji da ‘yan sandan Najeriya sun kashe wasu ‘yan IPOB a Abia da Enugu.
Majalisar dokokin jihar Ondo tace ko kaɗan bata da niyyar tsige mataimakin gwamnan jihar.
Kotu ta bada belin matar da ta kwarara wa makwabciyar ta ruwan barkono a Abuja.
Mahukunta a Abuja sun kama ƴan iskan gari mutum 400 da motoci 50 da suka karya doka.
Dan majalisa mai ci a jihar Ribas, Honarabul Dinebari Loolo ya rasu jiya Litinin.
Wani jami’in hukumar kiyaye haɗura ta kasa (FRSC) ya riga mu gidan gaskiya a wani hatsarin da ya auku a jihar Legas.
Amurka da Iran sun yi musayar fursunoni a karkashin jagorancin Qatar.
Tarayyar Turai na goyon bayan jakadan Faransa da aka yi ‘garkuwa’ da shi a Nijar da Bazoum.
UNESCO ta saka tsohon garin Gordion na Turkiyya a jerin kayan tarihi na duniya.
Babbar jam’iyyar adawa a Masar ta ce za ta kauracewa zaɓen shugaban ƙasar.
Amurka ta nemi mutane su taimaka wajen gano jirgin yaƙinta na dala miliyan 100.
Tsohon shugaban ƙasar Zambia Edgar L. ya shigar da gwamnatin ƙasar ƙara gaban kotu sakamakon haramta masa halartar taro a Koriya ta Kudu.
Masu aikin haƙar ma’adanai 20 sun mutu a haɗarin mota a Afrika ta Kudu.
Daruruwan mutane suna zanga-zanga a Libya kan zargin hukumomi da yin watsi dasu bayan mummunar ambaliyar ruwa ta tagayyara su inda ta kashe dubban mutane.
Pep Guardiola ya ce ba wani siddabaru yake yi ba a Manchester City da har ya lashe Champions League a karon farko.
EPL: Burnley da Nottm Forest sun tashi 1:1 a wasan jiya.
Laliga: Girona sun sami nasara akan Granada da ci 4:2 a wasan jiya.