Afghanistan: An tashi a yanayi na rashin tabbas
Kungiyar Taliban ta ce ta yi nasara a Afghanistan bayan da ta kame babban birnin kasar Kabul, abin da ya kawo cikin gaggawa karshen kusan shekara ashirin na iko da kasancewar sojojin hadaka da Amurka ta jagoranta a kasar, da kuma gwamnatin da suka jagoranci kafawa.
Ana ganin yadda mayakan kungiyar suka kama iko da fadar shugaban kasar, wanda ya tsere. Mai magana da yawun kungiyar ya ce an kawo karshen yakin.
Babban birni, Kabul wanda shi ne ya kasance na karshe a cikin manyan birane na Afghanistan da mayakan kungiyar suka kama, a mamayar da suka fara kusan kwana goma baya,
shekara kusan ashirin da Amurka ta jagoranci hambarar da su daga mulki, ya kasance cikin rudani bayan da fadar mulkin kasar ta shiga hannunsu, sauran manyan gine-gine na hukumomin gwamnati suka kasance karkashin ikon kungiyar kamar.
Mazauna birnin da ‘yan kasashen waje na ta in-ba-ka-yi-ban-wuri a kokarinsu na ficewa daga kasar.
Wasu ‘yan kasar kuma samun kansu a wannan yanayi na rashin tabbas, sun hakura tare da zuba wa sarautar Allah ido kan yadda rayuwarsu za ta kasance a karkashin ikon Taliban a wannan karon.
Kamar yadda wani ganau ya sheda wa BBC, a babban filin jirgin saman Kabul, ma’aikata sun yi watsi daga wuraren da suke, yayin da jama’a ke gudu don su shiga jirage.
Sai dai wasu rahotanni na cewa an dakatar da harkokin tashin jiragen kasuwa yayin da ake kokarin kwashe sauran sojojin kasashen waje.
Daman Taliban ta kama iko da birnin bayan yawancin sojojin taron-dangi sun fice.
Wata sanarwa da ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta fitar ta ce, Amurkar ta mayar da dakarunta domin su tsare filin jirgin saman na Kabul tare da sojojin kungiyar Nato.
Sojojin nata su kusan dubu shida an ce su ne za su karbi aikin sauka da tashin jiragen in ji sanarwar.
Kasashen waje na bayar da fifiko wajen kwashe jami’an diflomasiyyarsu da ‘yan kasashensu daga babban birnin.
Amma kuma Amurka ta ce, ita za ta hada har da ‘yan kasar ta Afghanistan da suka yi mata aiki, kamar tafintoci, da sauran ‘yan kasar masu rauni wadanbda suka cancanci samun bizar ‘yan gudun hijira.
Cikin dare an sauke tutar Amurka a ofishin jakadancin kasar a Kabul, abin da ke nufin kawo karshen kwashe ma’aiakata daga ofishin.
Rahotanni sun nuna cewa kusan dukkanin ma’aikatan ofishin tuni suna babban filin jirgin sama na birnin, suna jiran a kwashe su.
Matakin shugaba Joe Biden na janye sojojin kasarsa daga Afghanistan din da ya bude kofar sake kuuno kai da har aka kai ga wannan gaba da Taliban din ta sake kwace iko, bai sa shugaban nadama ba.
Shugaban Biden ya bayyana kwarin guiwarsa a kan dakarun Afghanistan din 300,000 da aka bari da cewa za su iya kare kasarsu a karshe-karshen makon da ya gabata.
A yayin da ita kuwa Taliban take da zaratan mayakan da aka kiyasata sun kai kusan dubu hamsin zuwa dari daya.
Wannan ne ya sa nan da nan mayakan na Taliban suka shiga karbe birni bayan birni, da lardunna, a rashin taimakon sojin Amurkar da dakarun na Afghanistan suka saba samu.
Jami’an tsaro suka bace daga shingayen tsaro, wasu sojojin ma suka tsere abinsu kawai aka rasa su.
A ranar 6 ga watan nan a Agusta Taliban ta kama birni na Zaranj, daga nan cikin kwana goma, suka kama dukkanin manyan biraden larduna goma, sannan a yanzu suka kama Kabul.
Sama da kasashe sittin da suka hada da Amurka da Burtaniya, sun fitar da sanarwa ta hadin guiwa, suna nuni da cewa, al’ummar Afdghanistan sun cancanci zama cikin kwanciyar hankali da tsaro da kuma cikin mutunci,.
Kuma dole ne a tabbatar da dawo da tsarin bin doka da oda na lumana da kuma tsaro.
Kasashen sun kuma yi kira ga kungiyar Taliban da ta bar duk mai son fita daga kasar ya fice salin-alin, ta kuma bar tituna da filayen jiragen sama da kan iyaka a bude.