Al’umar karamar hukumar Birnin Gwari sun ce sabuwar kungiyar nan mai kama da ta Boko Haram da ake kira Ansaru na kara karfi a wasu sassan karamar hukumar kuma har shugabaanni ta sun hana mutanen yankin shiga harkokin zabe.
Kamar Yadda VOA ta wallafa, Kusan shekaru biyu kenan da fara yada labarin bayyanar kungiyar Ansaru a wasu sassan kananan hukumomin Birnin Gwari da Igabi a jahar Kaduna kuma ya zuwa yanzu ‘ya’yan kungiya da akidun ta ke kama da na Boko Haram ya fara shiga garuruwa don yada manufofin ta kamar yadda jagoran bincike kan matsalolin tsaro a Birnin Gwari, Malam Dayyabu Haruna baban Abba ya shedawa Muryar Amurka.
Ya ce a baya can ‘ya’yan kungiyar a cikin daji su ke rayuwa amma yanzu sun sami dama sun shiga garuruwa kuma su ke yadda su ke so saboda makaman da su ke rike da su. Ya ce sun fitar da sanarwa cewa ba su amince al’umar yankin su shiga harkar zabe ba.
Tuni dai masana harkokin tsaro irin su Manjo Yahaya Shinko mai ritaya ke ganin wannan kungiya ka iya kafa tutoci a wasu yankuna wannan kasa idan ba a dauki matakan gaggawa ba.
Manjo Shinko ya ce bai kamata gwamnati ta dauki al’amurran kungiyar ta Ansaru da wasa ba tun yanzu mutanen kauyuka sun fara musu mubaya’a.
Yanzu haka dai wasu al’umomi da ke kusa da inda ‘yan kungiyar ta Ansaru su ke zaune sun mika wuya saboda taimakon da su ke samu daga kungiyar kamar yadda Malam Dayyabu Harunan da ke yankin ya tabbatar, inda ya kara da cewa kariyar da ‘yan kungiyar ta Ansaru ke ba al’umomin yankin ne ke sa su na kara amanna da su.
Dama dai kananan hukumomin Birnin Gwari da Igabi na cikin masu fama da matsalolin tsaro saboda hare-haren ‘yan-bindiga sai kuma ga wannan sabuwar kungiya ta Ansarun da duk dai an ce bata cutar da mutanen yankin amma ana fargabar manufofin ta da mazauna yankin ke cewa irin na Boko Haram ne.