Kotun Nijeriya ta ɗaure shugaban ƙungiyar Ansaru shekara 15 kan ta’addanci

Kotun Nijeriya ta ɗaure shugaban ƙungiyar Ansaru shekara 15 kan ta’addanci

Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta samu Mahmud Usman, ɗaya daga cikin kwamandojin ƙungiyar ta’addanci ta Ansaru, da laifi tare da ɗaurin shekara 15 a gidan yari.

Usman, wanda aka fi sani da Abu Barra, hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta gurfanar da shi a gaban kotu, inda ya amsa laifin haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba. Takardar tuhumar ta nuna cewa wannan laifi ya ba shi damar sayen makamai domin gudanar da ta’addanci da garkuwa da mutane.

Alƙalin kotun, Maishari’a Emeka Nwite, ya bayar da umarnin a ci gaba da tsare shi a hannun DSS har zuwa lokacin da za a gudanar da shari’a kan sauran tuhume-tuhume 31 da ke kansa.

A cikin takardar ƙara mai ɗauke da tuhume-tuhume 32 da DSS ta gabatar, an haɗa Usman da Abubakar Abba wajen kai hare-haren ta’addanci a shekarar 2022, ciki har da harin da aka kai barikin sojin Najeriya na Wawa Cantonment a Kainji, Borgu LGA, Jihar Neja.

An kuma tuhume su da samun horo kan amfani da makamai da haɗa bama-bamai a sansanonin ’yan ta’adda, tare da samun ƙarin horo kan dabarun yaƙi daga wata ƙungiyar ta’addanci a ƙasar Mali.

Bayan ɗaurin shekara 15, Mai shari’a Nwite ya saka ranar 21 ga Oktoba a matsayin ranar shari’ar sauran tuhume-tuhumen da DSS ta gabatar.

Hukumar DSS ta kuma zargi Usman da jagorantar harin watan Yuli 2022 a gidan yarin Kuje da ke Abuja, inda aka kuɓutar da fursunoni fiye da 600. Haka kuma, an danganta shi da harin tashar wutar lantarki a Nijar da kuma garkuwa da Injiniya ɗan Faransa, Francis Collomp, a shekarar 2013.

Baya ga haka, Usman da ƙungiyarsa sun shiga cikin garkuwa da mutane da dama, ciki har da Alhaji Musa Umar Uba, Magajin Garin Daura, a 2019, da kuma jerin fashi da makamai.

Mai ba wa shugaban kasa shawara kan tsaro, Nuhu Ribadu, ne ya sanar da kama kwamandojin, inda ya bayyana cewa an yi nasarar hakan ne bayan haɗin gwiwar jami’an tsaro. Ribadu ya bayyana Usman a matsayin wanda ya ke kiran kansa “Amir” na Ansaru, wanda ya jagoranci ƙungiyar “Mahmudawa” kusa da gandun dajin Kainji.

Ƙungiyar Ansaru dai ta bayyana ne a watan Janairu 2012 bayan ta balle daga Boko Haram.