Kotun sauraren kararrakin zaben Majalisar tarayya da Jiha da ke zamanta a Kano a ranar Alhamis, ta tabbatar da nasarar Sagir Koki, na jam’iyyar NNPP, wanda Muntari Ishaq Yakasai na APC, yake kalubalen nasarar da ya samu a zaben Majalisar Wakilai Mai wakiltar karamar hukumar Birni wanda aka gudanar a ranar 25 ga Fabrairu, 2023.
A hukuncin da ta yanke, kotun mai alkalai 3, karkashin jagorancin Mai shari’a Flora Ngozi Azinge, sun tabbatar da cewa mai shigar da kara, Muntari Yakasai, ya kasa tabbatar da tuhumar da yake yiwa zaɓen koki, inda yace ba’a rashin tattara sakamakon zabe a rumfunan zabe 25 da ke mazabar ba, a lokacin zaben.
Justice watch news ta rawaito Kotun ta ce mai shigar da kara ya kasa tabbatar da tuhumar da ake yi masa na rashin bin ka’ida ta hanyar gabatar da gamsasun shaidu, don tabbatar da ikirarin nasa.
Hakazalika Kotun ta tabbatar da cewa shaidun da mai shigar da kara ya gabatar, basu da inganci.
“A cikin shaidun da suka bayar, shaidun sun tabbatarwa kotun cewa ba sa rumfunan zabe da ake zargin an yi aringizon kuri’u.
“Ya kuma gabatar da wasu takardu da ba su dace ba don tabbatar da zarge-zargen tafka magudi, kan zabe, da rashin bin dokar zabe, 2022.”
Kotun ta kuma umarci wanda yayi karar da ya biya wanda akai Kara Naira dubu 100 .