A ranar Laraba nan ne kotun shari’ar Musuluncin nan ta birnin Kano da ke Najeriya take sauraron ci gaba da shari’ar malamin nan na jihar Sheikh Abduljabbar Kabara.
An fara zaman ne da misalin karfe 9:20 na safiya a babbar Kotun shari’ar Musulunci da ke Kofar Kudu daura da gidan Sarkin Kano.
An sauya zaman kotun na yau inda duk da takaita yawan mutane domin rage cunkoso, lauyoyi sun cika kotun ba tare da lura da kiyaye dokar bayar da tazara ba.
A ranar 18 ga watan Agusta, Alkali Sarki Ibrahim Yola ya ɗage zaman shari’ar sakamakon hujjojin da ɓangarorin biyu suka gabatar.
Ranar Juma’a 16 ga watan Yuli ne gwamnatin jihar Kano ta gurfanar da malamin a gaban kotu bisa zargin ɓatanci ga addini da kuma tunzura jama’a, zargin da ya sha musantawa.