Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta bayyana ayyukan kungiyoyin ‘yan Bindiga da ‘Yan Ta’adda a matsayin ayyukan ta’addanci.
Alƙalin kotun Taiwo Taiwo, ya bayar da umarnin kan buƙatar da gwamnati ta shigar, kamar yadda jaridar TheCable ta ruwaito.
Ta ce daraktar shigar da ƙara na ma’aikatar shari’a ta tarayya Mohammed Abubakar, wanda ya shigar da ƙarar, ya ce shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da matakin, wanda manufarsa ita ce “ayyana da ‘Yan Bindiga da ‘Yan Ta’adda da sauran ƙungiyoyin ta’addanci a kasar.
Kuma a wasu bayanai da ya gabatar, gwamnatin Najeriya ta ce bayanan tsaro sun tabbatar da ƴan bindiga na kashewa da satar mutane da fyaɗe da sauran miyagun ayyuka a arewa maso gabashin Najeriya da yankin arewa ta tsakiya da kuma sauran sassan Najeriya.
“Lokacin da ya ke bayyana hukuncin a ranar Alhamis, kotun ta ayyana ayyukan ƴan bindiga da ƙungiyoyin ta’adda da sauran masu ɗauke da makamai a sassan ƙasar musamman a arewa maso yammaci da arewa ta tsakiya a matsayin ayyukan ta’addaci.”