Kotu ta ƙi bayar da belin ɗan fitaccen jarumin fina-finan Indiya na Bollywood Shah Rukh Khan, kwana 18 bayan kama shi kan zargin mu’amala da miyagun ƙwayoyi a wajen wata liyafa.
An ɗauki Aryan Khan mai shekara 23 a cikin wani babban jirgin ruwa da ke kan hanyarsa ta zuwa jihar Goa daga birnin Mumbai ranar 2 ga watan Oktoba.
Hukunar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta tuhume shi a ƙarƙashin dokokin “mallaka da amfani da kuma sayar da miyagun ƙwayoyi.”
Ya yi watsi da dukkan zarge-zargen da ake yi masa.
Lauyansa Satish Manshinde ya sha nanata wa kotun cewa ba a samu komai a tare da ɗan jarumin ba, “kuma babu wata shaida da ke nuna cewa ya sha wata muguwar ƙwaya.”
Amma wata kotu a Mumbai a yau Laraba ta yi watsi da batun ba shi beli a karo na biyu. Ta fara watsi da batun ba da belin nasa ne ranar 8 ga watan Oktoba.
Sannan kotun ta ƙi bayar da belin wasu sauran mutum biyu da su ma ake tuhumarsu.
Ana sa ran lauyoyin Aryan Khan za su ɗaukaka ƙarar matakin a babbar kotun Mumbai.