X

Kashe wata budurwa mai shekara 17 a Iran da wani mutum ya yi ya jawo zazzafar muhawara

Kashe wata budurwa mai shekara 17 a Iran da wani mutum da aka ce mijinta ne ya yi ya jawo zazzafar muhawara kan dokokin da suke zagaye da batun “kisan gudun abin kunya” a ƙasar da kuma yadda ake ruwaito su a kafafen yaɗa labarai.

Gargaɗi: Wannan maƙalar na ƙunshe da wasu bayanai masu ɗaga hankali 

Wani bidiyo da ke nuna yadda wani mutum ke riƙe da wuƙa a hannu yayin da ya riƙe kan mace da ɗaya hannun, ya yadu kamar wutar daji a shafukan sada zumunta har ma aka dora shi a kan shafin intanet na kafar labaran Iran wato Rokna.

Sai dai daga baya hukumomi sun rufe shafin intanet din na Rokna.

Me ya faru?

Rahotanni na cewa lamarin ya auku ne a birnin Ahvaz da ke lardin Khuzestan a kudu maso yammacin Iran ranar Asabar 5 ga watan Fabrairu.

Kamfanin dillancin labarai na Iran, Rokna ya wallafa rahoton da ke cewa mijin yarinyar ce mai shekara 17 da haihuwa ya kashe ta kuma ya datse kanta.

Amma wasu rahotannin na cewa iyalanta ne suka je Turkiyya kuma suka mayar da ita gida Iran.

Wani bidiyo ya nuna mijin yarinyar yana yawo a titunan birnin Ahvaz dauke da kan matar tasa kafin ‘yan sanda suka kama shi. An rika yada bidiyon a shafukan sada zumunta.

Washegari kuma kamfanin dillancin labarai na ILNA ya ce an kama wasu ‘yan uwa su biyu bayan kisan, kuma sun ce su ne suka datse kan yarinyar.

Kamfanin dillancin labarai na ILNA ya ce jami’in ‘yan sanda Kanar Sohrab Hosseinnejad ya bayyana lamarin kamar haka: “An mika su ga bangaren shari’a.”

Kafofin yada labarai na garin sun ce hukumomi na tuhumar mutumin tare da dan uwan nasa “kan aikata kisan matar mutumin,” kuma “da alamu matsalolin cikin gida ne dalilan kisan.”

Me iyalan wadda aka kashen ke cewa?

Mahaifin Mona ya gana da kamfanin dillancin labarai Entekhab.

A cikin hirar ya ce ya tafi Turkiyya da mahaifin mijin Mona domin su koma da ita birni Ahvaz a kudancin Iran.

Mahaifin Mona ya ce wata kungiyar masu aikata laifi ne suka dauke ‘yar tasa daga Ahvaz zuwa Tehran, daga nan suka kai ta Turkiyya. Ya ce wani mai garkuwa da mutane dan Syria da ke Turkiyya ya bukaci su biya shi kudin fansa kafin ya sake ta.

Mahaifin Mona ya ce tun tana karama ya amince zai aurar da ita ga mijin nata Sajjad, sai dai ya ce babu kanshin gaskiya cewa tana son kashe aurenta.

Ya kuma ce ya shigar da kara a kotu kan kashe ‘yarsa da datse mata kai da sajjad yayi, kuma ba zai yafe ma sa ba.

Martanin da kisan ya haifar

Mutane masu yawa sun yi tir da kisan kan, kuma sun yi amfani da alamar #Ahvaz, #honour_killing da #child_marriage a Twitter domin bayyana rashin jin dadinsu kan batun.

Kisan shi ne babban labarin da dukkan jaridun Iran suka wallafa.

Dubun-dubatan ‘yan Iran sun kalli bidiyon da kamfanin dillancin labarai na Rokna ya wallafa a shafukan sada zumunta da ma shafinsa na intanet.

Me dokokin Iran ke cewa kan ‘kisan gudun abin kunya’?

A Iran, kundin shari’ar kasar na rage karfin hukuncin da ake yanke wa iyaye maza ko mahaifin da aka samu da laifin kisan ‘ya’yansu ko kuma abin da ake kira “kisan gudun abin kunya”.

Kundin shari’ar ya cire wannan rukunin mutanen daga hukuncin kisa idan aka same su da kisan ‘ya’yansu ko jikokinsu.

Me yasa ake aikata ‘kisan gudun abin kunya’?

Kisa ne da wani dan uwa ke aikata wa kan wani dan uwansa ko ‘yar uwarsa idan aka ga sun aikata wani abin da iyalinsa ke kallo a matsayin abin kunya ne.

Akwai wasu dalilian da suka hada da:

  • Kin amincewar mace ta auri mutumin da aka samo ma ta
  • Kasancewa an taba yi wa mace fyade
  • Ta aikata zina, ko da kuwa zato ne kawai

Wani dalilin ya hada da sanya kayan da basu dace ba da nuna halayyar da ake kallo a matsayin ta bijire wa magabata.

Categories: Labarai
twinsem2:
X

Headline

You can control the ways in which we improve and personalize your experience. Please choose whether you wish to allow the following:

Privacy Settings