Ministan harkokin ƴan sanda, Mohammed Dingyadi ya ce Naira biliyan 871.3 da aka ware domin gudanar da ayyukan ƴan sanda a cikin kasafin kudin 2023 ba zai isa ba.
Dingyadi ya bayyana haka ne a Abuja a yau Talata lokacin da ya ke jawabi a taron kare kasafin kudin shekarar 2023 wanda kwamitocin majalisar dattawa da na wakilai na majalisar dokokin kasar kan harkokin ƴan sanda su ka gudanar.
Jaridar DAILY NIGERIA ta wallafa cewa Ministan ya ce kasafin kudin da aka ware wa ma’aikatar da hukumominta domin tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyi ba zai isa ba.
Dingyadi ya ce daga cikin jimillar Naira biliyan 871.3 da aka ware a kasafin kudin shekarar 2023, Naira biliyan 3.52 na ayyukan babbar ma’aikatar ne.
Ya ce an ware wa rundunar ‘yan sandan Najeriya Naira biliyan 805.5.
Ministan ya ce makarantar horar da ‘yan sanda za ta samu Naira biliyan 5.17, yayin da asusun kula da ‘yan sandan Nijeriya ya samu Naira biliyan 57.14, wanda ya kai Naira biliyan 871.3