Wani hadarin kwale kwale a Jihar Kano da ke Najeriya ya yi sanadiyyar mutuwar dalibai 20 a yammacin Talatar nan cikin karamar hukumar Bagwai, yayin da aka ceto wasu guda 7 da ran su.
Bayanan dake zuwa daga yankin sun ce kwale kwalen na dauke da mutane 47 wadanda akasarin su daliban makarantar Islamiya ne dake kauyen Badau akan hanyar su ta zuwa Bagwai domin halartar taron Maulidi.
Mai Magana da yawun hukumar agajin gaggawa ta jihar Kano Saminu Abdullahi yace an samu hadarin ne da misalin karfe 9.15 na dare, kuma gawarwaki 20 kawai aka iya tsamowa daga ruwan.
Jami’in ya kara da cewar an yi nasarar ceto mutane 7 da ran su daga hadarin, yayin da ake ci gaba da neman sauran daliban.
Wannan hadari ya girgiza jama’ar yankin da jihar Kano baki daya.