Tsohon shugaban kasa na mulkin soja, Janar Ibrahim Badamasi Babangida, IBB (rtd) ya yi kira ga ‘yan Najeriya da kada su karaya, yana mai cewa da addu’a da hakuri, halin da ake ciki yanzu zai zama tarihi.
Janar Babangida ya bayyana haka ne a lokacin da mambobin kungiyar ‘yan jarida ta Najeriya reshen jihar Neja karkashin jagorancin shugaban kungiyar Mustapha Bina suka kai masa ziyara a gidansa da ke kan tudu domin taya shi murnar cika shekaru 81 a duniya.
Ya ce, “Bai kamata ‘yan Najeriya su yi kasa a gwiwa ba game da kalubalen da kasar ke fuskanta domin hakan ma zai wuce.”
A cewarsa, “Ku ‘yan jarida ku yi watsi da ‘yan siyasa da daidaikun mutane masu wa’azin kiyayya da rashin hadin kai a yayin da yakin neman zabe ke kara karatowa a zaben 2023.
“Ina rokon mu da mu yi hakuri da juna kuma mu kasance masu yin addu’a. Muna bukatar mu ci gaba da wayar da kan jama’a kan yadda za a yi zaman lafiya da lumana, ina kuma rokon wadanda suke da hannu a cikin jerin matsalolin rashin tsaro a fadin kasar nan da su canja tunani.”
Ya bukaci ‘yan Najeriya da su ci gaba da yin imani da hadin kan kasar, kuma su kasance masu nagarta da kuma dagewa cewa Najeriya za ta samu sauki.
Ya ce a matsayinsa na ’yan jarida, “Za ku iya yin hakan ne kawai ta hanyar bayar da rahoto na gaskiya kuma ina son muhawarar da ke gudana a kafafen yada labarai, tana baiwa jama’a basirar da ya kamata su gani.
“Abin da kuke yi a yanzu ya isa ya inganta hadin kan kasa kuma har yanzu kuna iya canza tunanin ‘yan Najeriya don haka ina rokon ku da ku yi watsi da masu wa’azin kiyayya da rashin hadin kai. Yi watsi da su kuma kada ku damu da su.”
A lokacin rayuwarsa yana da shekaru 81, tsohon Shugaban na Soja ya ce: “Na gode wa Allah da ya sa ni cikin wadannan shekaru.
“Darussan da na koya tsawon shekaru da suka yi min shine hakuri, imani da mutunta kowane dan Adam kuma ya kamata ’yan Najeriya su koyi yin kwatankwacin wadannan kyawawan halaye. “