Kwanaki sha biyar da kai harin jirgin kasan Abuja-Kaduna, ‘yan uwan mutanen da aka sace sun ce lokaci ya yi da gwamnati ya kamata ta nemawa wadanda aka kama mafita tunda ‘yan bindiga sun ce da gwamnati za su yi Magana.
Sauya sabon salon sakin faya-fayan bidiyo masu dauke da wadanda aka yi garkuwa da su a harin jirgin kasan Abuja-Kaduna dai ya tada hankalin ‘yan uwan mutanen da aka sace har ma wasu daga cikin su na baiwa gwamnati wa’adin sa’o’i 72 ta dauki matakin karbo ‘yan uwansu ko kuma su shiga dajin da kansu.
Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasuru Ahmed El-rufa’i ya ruga fadar shugaban kasa game da wannan matsala ta tsaro kuma tun a lokacin ya sanar da cewa akwai alamu sai gwamnati ta sa baki.
Maganar sulhu da ‘yan bindiga dai na cikin abubuwan da wasu ke ta kwadaitarwa, kuma Dr. Ahmad Gumi ya ce ita ce babbar mafita.
Yanzu dai kusan faya-fayan bidiyo uku ke nan ‘yan bindigan da su ka kaiwa jirgin kasan hari su ka fitar kuma a ciki ne su ke ta jaddada cewa gwamnati ta san abun da su ke nema.