Sabon jirgin yaƙin rundunar sojin Najeriya na Super Tucano ya tarwatsa mayaƙan ISWAP tare da lalata motocinsu na igwa a Gajiram da ke jihar Borno a arewa maso gabashin Najeriya.
Kafar yaɗa labaran PRNigeria ta ce masu tayar da ƙayar bayan sun shiga garin a cikin motocin yaƙi da zummar kai masa hari, sai jirgin yaƙin ya isa wajen.
Rundunar sojin Najeriya ta ce ta ƙwato makamai da dama a yayin da dakarun sama da na ƙasa suka fatattaki mayaƙan.
PRNigeria ta ce wani jami’in leƙen asiri na soja ya ce a ƙalla an ga gawarwarki 26 na mayaƙan bayan hare-haren saman.
“Jirgin yaƙin ya isa wajen a daidai lokacin da mayaƙan suka je garin inda ya fatatteke su tare da hallaka su suka ƙone yadda ba a iya gane su.
“Zuwa yanzu mun ƙirga gawarwaki 26 na ƴan ta’addan amma abin takaici mun rasa sojoji biyu a yayin da suke tunkarar maƙiyan namu.
“Ana iya hango wasu gawarwakin ƴan ta’addan daga can nesa a cikin motocinsu da ke cin wuta a kan hanyar ƙauyen Kunli da ke gabashin garin,” in ji jami’in.
A watan Yuli ne Najeriya ta karɓi jiragen yaƙi samfurin Super Tucano da ta saya a hannun Amurka da nufin yaƙi da matsalar rashin tsaro a arewa maso gabashin ƙasar da sauran sassan da ke da irin wannan matsala.
Jirgin Super Tucano yana aikin tattara bayanan sirri da sa ido da kai harin sama da ƙasa, kuma ƙwararu sun ce zai taimaka wa ƙasar yin yaƙi da ta’addanci.
A watan Oktoba ne bayanaisuka yi ta yaɗuwa kan dalilan da suka sa aka ɗauki lokaci bayan sayen jiragen ba a fara amfani da su ba.
Hakan ya faru ne ganin cewa tun bayan isar jiragen Najeriya ƴan ƙasar da dama sun saka ran cewa nan da nan za a fara amfani da su wajen kai wa ƴan fashin daji hare-hare don murƙushe su, musamman a yankunan arewa maso yamma da arewa ta tsakiya.
Sai dai rahotanni sun ce akwai wani babban lamari da ke jawo tsaiko wajen aiwatar da hakan, wanda bai wuce sharaɗin da ke dabaibaye da sayen jiragen ba tun farko, wanda Amurka ta sanya.
Tun lokacin sayen jiragen dai rundunar Sojin Najeriya ta shaida wa Majalisar Dokokin ƙasar cewa, tun farko Amurka ta yarda ta sayar da jiragen yaƙi na A-29 Super Tucano 12 ne idan za a yi amfani da su a kan ƴan ta’adda da masu tayar da ƙayar baya ne kawai, ban da ƴan fashin daji.
Wato hakan na nufin duk wadanda ba a ayyana su a matsayin ƴan ta’adda ba to ba za a yaƙe su jiragen ba.
Kamfanin kera jiragen sama na Embraer S.A na kasar Brazil ne ke kera samfurin jiragen na Super Tucano A-29.
A watan Disambar shekarar 2018 ne kamfanin na Embraer da abokin huddarsa na kasar Saliyo Nevada Corporation (SNC) suka samu kwangilar sayen jirage 12 na A-29 Super Tecano daga Rundunar Sojin Saman Najeriya NAF.
Kwangilar ta kuma ƙunshi kayayyakin horarwa daga kasa, da na’urorin tsara ayyukan soji, da sauran kayayyakin aiki ga rundunar sojin saman ta Najeriya.
Tun a lokacin mulkin tsohon shugaban Amurka Barack Obama ne gwamnatinsa ta bukaci amincewar sayar da jirgin yakin na Super Tucano ga Najeriya don taimaka mata wajen yaki da kungiyar Boko Haram.