Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya ware naira biliyan 1.3 ga daliban ma’aikatan jinya da ungozoma 997 wadanda ‘yan asalin jihar ne.
Gwamnan ya bayyana hakan ne jiya a yayin kaddamar da shirin bayar da tallafin karatu a Maiduguri babban birnin jihar.
Ya ce da farko shirin ya samu ‘yan takara 1,080, inda aka zabo ‘yan takara 40 daga kowace karamar hukuma 27.
Bayan jarrabawar shiga jami’a, an zabi ‘yan takara 997 da suka yi nasara don cin gajiyar tallafin.
Zulum ya jaddada cewa wannan shiri na da nufin magance karuwar bukatar ma’aikata na ayyukan kiwon lafiya saboda karuwar al’ummar jihar.
Kasafin kudin tallafin, ya ce ya hada da N124,149,000 na kudin makaranta, yayin da sauran Naira miliyan 1,181,040,000 za a biya a matsayin alawus na Naira 30,000 duk wata ga kowane dalibi a duk tsawon karatunsa.