Jarumin jarumi Usman Baba Pategi wanda aka fi sani da Samanja Mazan Fama ya rasu yana da shekaru 84 a duniya. Shahararren jarumin fina-finan Hausa na Kaduna ya rasu da misalin karfe 12:15 na safiyar Lahadi.
Daya daga cikin ‘ya’yansa, Mohammed Usman, ya tabbatar da rasuwarsa ya bayyana cewa mahaifinsa ya bar mata biyu. Ya rasu yana da shekaru 84 kuma ya bar mata biyu da ‘ya’ya 12.” A cewar Mohammad, za a yi sallar jana’izar da karfe 10 na safe a wani masallaci da ke Kabala Costain Kaduna.