X

Jam’iyar Labour ta tsayar da Peter Obi ɗan takarar shugaban ƙasa

Tsohon gwamnan jihar Anambra, Peter Obi, ya zama dan takarar shugaban kasa na jam’iyar Labour (LP) a zabukan 2023 da ke tafe.

Ya sami nasarar ne a yau Litinin a wajen zaben fidda gwani da kuma babban taron jam’iyar da ke gudana a Asaba, babban birnin jihar Delta, bayan janyewar Pat Utomi wani tsohon mai bai wa shugaban kasa shawara.

A makon da ya gabata ne Peter Obi wanda jam’iyar PDP ta tantance dontakarar kujerar shugaban kasa ya fice daga jam’iyyar, yana mai cewa bai ji dadin abubuwan da ke faruwa a cikin jam’iyyar ba a baya-bayan nan, wadanda sun yi sabani daka’idojinsa, don haka ya yanke shawarar ficewa daga jam’iyyar.

Categories: Labarai
twinsem2:
X

Headline

You can control the ways in which we improve and personalize your experience. Please choose whether you wish to allow the following:

Privacy Settings