X

Jami’an tsaron Isra’ila sun bindige ‘yar jarida Shireen Abu Aqleh

Jami’an tsaron Isra’ila sun bindige Shireen Abu Aqleh , wata ‘yar jarida da ke aiki da tashar talabajin ta Aljazeera, daidai lokacin da take kan aikinsa kusa da sansanin ‘yan gudun hijirar Jenin da ke gabar Yammacin Kogin Jordan na Falasdinu.

Tashar talabijin ta Aljazeera da kuma ma’aikatar yada labara labaran Falasdinu sun tabbatar da mutuwar ‘yar jaridar sakamakon harbi da bindiga.

Hukumar FIJ ta fitar da alkaluma

Kungiyar kare ‘Yan jaridu © AFP – FETHI BELAID

Rahotanni daga hukumar yan jaridu ta Duniya FIJ, a shekara ta 2021 akalla ‘yan jaridu 47 ne aka kashe a Duniya,yayinda a shekarar da ta gabata an samu mutuwar ‘yan jaridu 65.

Hukumar na ci gaba da kir aga hukumomin kasashen Duniya na ganin sun bayar da kariya da ta dace don kare ‘yan jaridu a sassan Duniya.

Matakin da ga duk alamu bai yi tasiri ba ganin ta yada aka sake samun mutuwar ‘yar jaridar tashar talabijin ta Aljazeera.

Categories: Labarai
twinsem2:
X

Headline

You can control the ways in which we improve and personalize your experience. Please choose whether you wish to allow the following:

Privacy Settings