X

IVC: Ouattara ya gafarta wa Gbagbo

A wani yunkuri na samun zaman lafiya da hadin kan ‘yan kasa, shugaba a daidai lokacin da fagen siyasa ke daukar dumi, Shugaba Alassane Ouattara na Côte d’Ivoire ya yi wa Laurent Gbagbo ahuwa.

A cikin wani jawabinsa ga ‘yan kasar ta kafafen yada labarai mallakar gwamnati ne shugaba Alassane Ouattara ya bayyana matakin ahuwar ga tsohon abokin hamayyarsa, ya kuma umarci da a biya sa daukacin hakkokinsa da aka toshe na tsohon shugaban kasa shekaru 10 da suka gabata.

An zargi Laurent Gbagbo da laifin tada tsaune tsaye da ya yi sanadiyar asarar rayukan jama’a a babban zaben kasar na shekarar 2010, wanda har yakai ga kotu ta yanke masa hukuncin dauri na tsawon shekaru a gidan yari.

A watannin da suka wuce ne tsohon shugaban kasar ya koma gida, bayan da kotun ICC ta wanke shi daga zargin aikata laifin cin zarafin bani Adama.

Categories: Labarai
Tags: HAUSAlabarai
twinsem2:
X

Headline

You can control the ways in which we improve and personalize your experience. Please choose whether you wish to allow the following:

Privacy Settings