Isra’ila ta ci gaba da kai hare-hare kan birnin Khan Younis da ke kudancin Gaza wanda ya tilastawa dubunnan fararen hula ci gaba da kaura zuwa Rafah da ke gab da iyakar yankin da Masar, hare-haren da ke zuwa duk da hukuncin kotun duniya da ya bukaci kasar ta Yahudu ta tabbatar da kare rayukan fararen hula
Isra’ila ta yi umarnin gaggauta kwashe ilahirin majinyatan da ke asibitin Nasser cibiyar lafiya daya tilo mafi girma da ta rage a Gaza, baya ga wasu kananun cibiyoyin lafiya 2 da Isra’ilan ke sanar da shirin rushe su a hare-haren da sojinta za su kai.
Zuwa yanzu Falasdinawa akalla miliyan 1 da rabo kwatankwacin kashi 2 bisa 3 na al’ummar Gaza ne suka bar matsugunansu yayinda suke rayuwa a sansanonin wucin gadi ba tare da abinci ruwan sha ko kuma kulawar lafiya ba.
Haka zalika alkaluman mutanen da Isra’ila ta kashe zuwa yanzu ya zarta dubu 26 baya ga jikkata wasu dubbai.