Hukumar INEC ta Najeriya na wani zama na musamman don tattaunawa a kan makomar zaɓen gwamnan da za a yi a jihar Anambara, a watan Nuwamba mai zuwa.
Hukumar dai na nuna damuwa game da matsalar tabarbarewar tsaro a jihar, sakamakon hare-haren kungiyar IPOB a ofisoshin hukumar zaɓen da gwamnati.
Shugaban hukumar Farfesa Mahmud Yakubu ya bayyana cewa hukumar zaben ta damu sosai da yanayin da ta samu kan ta a jihar Anambra.
Farfesa Yakubu ya ce sun fahimci cewa babban burin maharan shi ne su hana yin zaɓe a Anambra.
Hukumar zabe ta nuna damuwa da abin da ya shafi kariyar ga lafiyar masu zaɓe da kuma malaman zabe da za su yi aiki a ranar zabe, ciki har jami`an tsaro, wadanda ke cikin mutanen da maharan ke nema.
Bayan haka akwai kayan zabe da za tura kananan hukumomin 21. Kenan kimanin jami`ai dubu 26 ne za su yi aiki.
Wannan na nuna girman kalubalen da ke gaban hukumar zabe.
Shugaban hukumar zaben ya bayyana cewa maharan sun lalata musu kayan aiki da ya shafi zaben. Amma ya ce hukumar ta yi nasarar maye gurbin kayan.
Shi ma mai bai wa shugaban kasa shawara a kan harkar tsaro, wanda wani darakta ya wakilta a wajen tattaunawar, ya ce gwamnatin tarayya ta dukufa wajen kare rayukan al`ummar Anambar da dukkan wadanda za su taka rawa a harkar zaben.
A cewarsa wannan ne ya sa sojin Najeriyar suka fara wani shiri na musamman a yankin don cimma wannan manufa.