X

“Ina da yakinin kotunan sama baza su tabbatar da wannan hukuncin ba” – Abba Hikima

Tun bayan yanke hukuncin zaben Gwabna na Jihar Kano da Kotun Turabunal ta yi Jama’a da dama suke ta fadin Albarkacin bakin su ciki Harda kwararren Lauyan nan Barr. Abba Hikima. Inda ya bayyana cewa

“Maganan nan fa daya ce. Idan za’a maka rashin adalci to sai kaga mutum ya zama wani iri. Sai ya ji yaki ji. Ya gani yaki gani. Ga abu a fili amma yaki fahimta. Ko kuma ga adalchi mai sauki amma sai an bi doguwar hanya domin a tabbatar da akasin sa.

Gaskiya ne. Akwai abubuwan da ni kaina ban gamsu da yadda aka tafi da su ba a shariar daga bangaren NNPP. Kuma tun farko na fada. Ana cikin shariar ma kafin azo ga6ar da kusan awa 2 na fadi tsorona.

Amma babu maganar rashin kwarewa a bangaren lauyoyin. Domin SAN 6 ne kuma gogaggu. Har wadanda ba SAN ba daga cikin team din babu wanda bai san shariar zabe ba daidai gwargwado.

Saboda haka da girmamawa ga kotu, bai kamata ace wannan hukuncin aka gabatar ba a fahimta ta.

Ina da yakinin kotunan sama baza su tabbatar da wannan hukuncin ta. Za’a samu sauki”.

Categories: Labarai
twinsem2:
X

Headline

You can control the ways in which we improve and personalize your experience. Please choose whether you wish to allow the following:

Privacy Settings