Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya, ya ce yaran kasar miliyan 12 ne ke cikin firgici da damuwa game da zuwa makaranta, sakamakon yawan sace-sacen jama’a don neman kudin fansa a kasar.
Shugaban ya bayyana hakan ne a yayin da yake bude shirin nan na inganta tsaro ga makarantu, wanda aka bullo da shi da nufin kyautata tsaro a makarantun yankin arewacin Najeriyar.
Yawan hare-hare da ake kai wa makarantu da dalibai a jihohin arewa maso yammacin Najeriya dai ya kassara karatu a yankin wanda dama ya jima yana fama da matsalar nagartaccen ilimi.
Yanzu haka dai, akwai dalibai da dama da ke zuwa makaranta cikin firgici, da wadanda ba sa ma zuwa makarantar, da kuma wadanda gaba daya sun yake kaunar zuwa makarantar, saboda matsalar ta tsaro.
Firgicin da ɗaliban da ake sacewa ke shiga
To sai dai ba a rasa wasu iyayen da ke yin ƙundumbala wajen tura ƴaƴansu makaranta, amma suna cewa suna yin hakan ne cikin dar-dar, domin ba su da tabbacin abin da ka je ya zo.
Wani mahaifi da ya bukaci mu sakaye sunansa, ya shaida wa BBC cewa ”Kullum abu dar-dar yake kawo mana, amma tunda zuwa makaranta ya zama dole to ya za mu yi ?. inji shi.
Ya ce ”Har sai mun ga sun dawo hankalinmu ke kwanciya, idan kuwa lokacin tashinsu ya wuce bamu ga sun dawo ba, to shikenan sai ka ga babu mu babu kwanciyar hankali har sai mun ga sun dawo gare mu.
Shi ma wani mahaifi da dansa ke cikin yaran da aka sace a makarantarr Bethel Bepist da ke jihar Kaduna ya ce bayan sako yaran da ƴan bindiga suka yi, sai dabi’un aronsa suka canja, ya dawo yana wasu abubuwa kamar ƙwaƙwalwarsu ta dan taɓu.
”Haka kawai sai ka ga ya firgita, ko da kuwa da abokansa yake wasa, wani lokacin kuma sai ka ga ya zauna shi kadai, ko kuma ya rika wasa shi kadai, muna ganin matsalar ta shafi tunaninsa, don ko sunan makaranta aka kira sai ka ga baya jin daɗi, kai hatta Kaduna da ya je karatu ɗin ma ko kaɗan ba ya son ya ji an kira sunan” inji wannan uba.
”Bazan sake zuwa makaranta ba”
Ita kuwa wata ɗaliba marainiya ƴar shekara goma sha uku da ta daina karatu saboda harin da ƴan bindiga suka kai wa makarantarsu hari ta shaida wa BBC cewa ta haƙura da karatun, domin ba za ta iya sake komawa ba.
”Hari aka kai mana da bindigogi, a makaranar gaba ɗaya kowa ya watse, lokacin mahaifina ya rasa rabsa domin garin aka kai hari ba kan makaranta kawai ba. bayan an gama zaman makoki sai muka koma wajen ƙanin mahaifinmu, shima da aka sake kawo wani hari ya fita gona shima ɗin aka kashe shi, sai gida aka kawo gwar shi” inji ta.
Wannan ɗaliba ta ce ko sunan makaranta ta ji an kirawo kanta ciwo yake yi, don haka ta haƙura da karatun baki ɗaya ba za ta iya sake komawa don ci gaba da yi ba.
Hare-haren da ƴan fashin daji ke kai wa makarantu suna sace ɗalibai dai sun kara kassara ilimin yankin wanda dama masharhanta ke cewa na tattare da koma baya.