X

ICAN ta musanta batan N80bn

Cibiyar da ke kula da Akantoci na Najeriya, ICAN, ta nisanta kanta daga dakatarwar Akanta-Janar na Tarayya, Alhaji Ahmed Idris, bisa zargin batan kudade Naira biliyan 80, biyo bayan wata wasika da kungiyar kare hakkin bil’adama da muhalli, HEDA ta aike da bukatar a gudanar da bincike tare da sanya mata takunkumi.

A wata sanarwa da babban magatakardar ICAN, Farfesa Ahmed Kumshe, ya sanyawa hannu, ta bayyana cewa: “An jawo hankalin ICAN kan wasu rubuce-rubucen da ake yadawa a kafafen yada labarai inda wata kungiya mai suna HEDA ke neman ICAN ta binciki tsohon Akanta tare da hukunta shi. – Hukumar Yaki da Yiwa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati, EFCC, na tuhumar Janar na Tarayyar Najeriya da laifin almundahana.

“Muna so mu sanar da kungiyar da sauran jama’a cewa tsohon Akanta-Janar, Alhaji Ahmed Idris, ba dan kungiyar ICAN ba ne, don haka ICAN ba za ta iya bincike da kuma hukunta shi ba.

“Aikinmu kawai yana ba mu damar daidaitawa da ladabtar da membobinmu lokacin da suka yi kuskure a Kwamitin Bincike ko Kotun ladabtarwa kamar yadda lamarin ya kasance.

“Mun yaba da damuwar HEDA kuma muna fatan mu tabbatar wa jama’a da sauran masu ruwa da tsaki kan kudurinmu na biyan bukatun jama’a a kodayaushe.

Categories: Labarai
Tags: HAUSAlabarai
twinsem2:
X

Headline

You can control the ways in which we improve and personalize your experience. Please choose whether you wish to allow the following:

Privacy Settings