Hukumar da ke Kula da Matasa Masu yi wa Ƙasa Hidima (NYSC) ta ce daga yanzu za ta hana duk matasa da basu yi rigakafin Corona ba shiga sansanoninta na ba da horo.
Shugaban hukumar, Birgediya Janar Shu’aibu Ibrahim, wanda ya sanar da hakan ya ce matakin zai fara aiki ne lokacin da za a bude sansanin ba da horo na gaba a makonni masu zuwa.Ya ce daga yanzu, dole matasan su nuna shaidar rigakafin kafin a yi musu rajista a sansanonin hukumar.
Birgediya Janar Shuaibu ya ce hukumar na kokarin yin taka-tsan-tsan ne wajen ganin ba ta bar cutar ta dada yaduwa ba, musamman ma yanzu da samfurin Omicron ya bulla a Najeriya.
Sai dai ya ce daga yanzu ba za a sake ba matasan hutun mako biyu ba bayan kammala karbar horo a sansanoni, inda ya shawaresu da su koyi sana’a ba tare da sun dogara da ayyukan gwamnati ba.
Ya kuma gargadi matasan da su kiyayi tafiye-tafiye da daddare, saboda kalubalen tsaro.
“Muna da dakunan kwanan matasa masu yi wa kasa hidima da sakatariya a kowacce jiha da barikokin sojoji, kamata ya yi ku tsaya ku kwana a can in kuka yi dare, kashegari ku ci gaba da tafiya,” inji Shugaban na NYSC.