X

Har yanzu ba a san adadin mutanen da ƴan bindiga suka sace ba a hanyar Kaduna zuwa Abuja

Har yanzu ba a san yawan mutanen da ke hannun ƴan bindiga ba bayan harin da aka kai kan hanyar Kaduna zuwa Abuja ba a ranar Lahadi. 

A ranar litinin gwamnatin Kaduna da rundunar ƴan sandan jihar ta ce ta ceto mutum 11 bayan musayar wuta da ƴan sanda da sojoji suka yi da ƴan bindiga.

Sai dai hukumomin har yanzu ba su tattance adadin yawan mutanen da aka sace ba. Jami’an sun samu motocin matafiya da dama ba kowa a cikinsu, wasu a cikin daji wasu kuma a gefen hanya.

Harin na hanyar Kaduna zuwa Abuja ya yi ajalin tsohon ɗan takarar gwamnan Zamfara Alhaji Sagir Hamidu.

Categories: Labarai
Tags: HAUSAlabarai
twinsem2:
X

Headline

You can control the ways in which we improve and personalize your experience. Please choose whether you wish to allow the following:

Privacy Settings