X

Hakainde Hichlema, ya lashe zaben shugabancin Zambia

Hakainde Hichilema Jagoran yan Adawa a kasar Zambia RODGER BOSCH AFP

Dan takarar adawa a zaben shugabancin kasar Zambia Hakainde Hichlema, ya lashe zaben shugabancin kasar  da aka gudanar ranar alhamis da ta gabata kamar dai yadda alkalumman hukumar zabe suka nuna.

Samarakon mazabu 155 daga cikin 156 da hukumar zaben ta fitar na nuni da cewa Hichilema ya samu kuri’u sama da milyan 2 da dubu 810 da kuri’u 757, yayin da shugaba mai-ci Edagar Lungu ya samu kuri milyan 1 da dubu 814 da 201 a wannan zabe.

Lura da wadannan alkalumma ne shugaban hukumar zaben kasar Esau Chulu ya tabbatar da Hichileme a matsayin zababben shugaban kasar Zambia.

Dan shekaru 59 a duniya, Hichilema wanda shahrarren dan kasuwa ne, ya yi nasarar doke shugaban da ke kan karagar mulkin kasar ne bayan ya tsaya takarar har sau 6, kuma 3 daga cikinsu yana karawa da shugaba Lungu.

A zaben da aka gudanar shekara ta 2016, duka duka an samu ratar kuri’u dubu dari daya ne a tsakanin mutanen biyu, sabanin wannan karo da aka samu tazarar kuri’u kusan milyan daya.

twinsem2:
X

Headline

You can control the ways in which we improve and personalize your experience. Please choose whether you wish to allow the following:

Privacy Settings