X

Hadakar Kwankwaso da Peter Obi Ta Fara Samun Ƙarfi

Punch ta wallafa cewa sakataren jam’iyyar LP, Umar Faruk ne ya tabbatar mata da amincewa da batun yin hadakar.

Maganar haɗakar Peter Obi da Kwankwaso A wata hira da Rabi’u Musa Kwankwaso ya yi, ya nuna zai amince da yin haɗaka da Peter Obi a zaben mai zuwa na 2027. Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya ce duk da ya fi Obi karfi a siyasa zai iya zama mataimakinsa idan aka cika wasu sharuda. Martanin LP kan haɗakar Obi da Kwankwaso Sakataren LP na kasa, Umar Faruk ya nuna amincewa da yin haɗaka tsakanin Kwankwaso da Peter Obi.

Umar Faruk ya ce jam’iyyar LP ta yi na’am da yardar Rabi’u Kwankwaso ya kasance mataimakin Peter Obi a zabe mai zuwa. Jam’iyyar LP ta ba Rabiu Kwankwaso shawara Jam’iyyar LP ta ce ya kamata Kwankwaso ya cigaba da ƙoƙarin tattalin maganar hadakar kada ya rudu da cewa yana da farin jini a Arewa.

Sakataren na LP ya kara da cewa Peter Obi ya samu kuri’u sama da miliyan 6 alhali Kwankwaso bai samu ko miliyan 2 ba wanda hakan zai sa Kwankwaso ya bi bayan Obi. Jigon APC ya yi watsi da hadakar yan adawa A wani rahoton, kun ji cewa tsohon kwamishina a jihar Kano, Musa Ilyasu Kwankwaso ya yi magana kan hadakar jiga-jigan jam’iyyun adawa game da zaben 2027. Iliyasu Kwankwaso ya ce Atiku Abubakar da Rabi’u Kwankwaso da Peter Obi suna bata lokacinsu ne kan shirin kifar da Bola Tinubu.

Categories: Labarai
twinsem2:
X

Headline

You can control the ways in which we improve and personalize your experience. Please choose whether you wish to allow the following:

Privacy Settings