X

Gwamnatin Najeriya ta saki Kanar Sambo Dasuki

Gwamnatin Najeriya ta saki Kanar Sambo Dasuki mai murabus, tsohon mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, bayan shafe sama da shekara hudu a hannun hukumomi.

An sake shi ne bayan sakin dan fafutukar nan mai jaridar nan ta Intanet, Sahara Reporters, Omoyele Sowore.

Kafin sakin nasu gwamnatin ta ja kunnen mutanen biyu da su kame daga aikata abubuwan da za su janyo tayar da zaune tsaye da kuma cikas ga tsaron kasa sannan kuma ka da su yi tarnaki ga shari’ar da ake yi musu bisa dokokin kasa

A karshen shekara ta 2015 ne gwamnatin Najeriya ta kama Sambo Dasuki bisa zargin karkatar da kudin makamai sama da dala biliyan biyu lokacin gwamnatin PDP, ta Goodluck Jonathan.

twinsem2:
X

Headline

You can control the ways in which we improve and personalize your experience. Please choose whether you wish to allow the following:

Privacy Settings