Gwamnatin Najeriya ta naɗa Anamekwe Chukwunyere Nwabuoku don ya maye gurbin Babban Akanta na Ƙasa Ahmed Idris, wanda aka dakatar saboda zargin almundahanar kuɗi da suka kai naira biliyan 80.
Wata sanarwa da fadar ta fitar a yammacin yau Asabar ta ce Mista Nwabuoku zai jagoranci ofishin babban akantan har zuwa lokacin da hukumar EFCC mai yaƙi da cin hanci za ta kammala bincikenta kan Ahmed Idris.
Mista Nwabuoku mai shekara 60 ya fito daga JIhar Imo da ke kudu maso gabashin ƙasar kuma shi ne darakta a ɓangaren kuɗi na ofishin akantan yanzu haka.
Jami’an EFCC sun kama babban jami’in gwamnatin ne ranar Litinin da ta wuce bayan ya ƙi amsa gayyata daban-daban da suka aika masa, a cewar hukumar.
EFCC na zargin Ahmed da halasta kuɗin haram ta hanyar sayen wasu kadarori a wurare daban-daban.