Rahotanni na cewa gwamnatin tarayyar Najeriya ta fara aiwatar da tsarin nan na ‘babu aiki, babu albashi’ kan malaman jami’o’in kasar da ke yajin aiki.
Idan ba a manta ba, kungiyar malaman jami’a a Najeriya ASUU ta tsunduma yajin aikin mako hudu a ranar 14 ga watan Fabrairu, wanda ta sabunta bayan ya kare.
Jaridar Vanguard ta ce shugaban kungiyar National Association of Academic Technologists Comrade Ibeji Nwokoma, ta malaman jami’a ya tabbatar cewa ba a biya mambobin kungiyar albashinsu na watan Maris ba.
Sai dai Mista Nwokoma ya ce wannan matakin na gwamnati ba zai hana su neman hakkokinsu ba.