X

Gwamnatin Jihar Kano Ta Dakatar Da Wanda ake Zargi Da Sayar Da Hatsin Jama’a

Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya bayar da umarnin dakatar da shugaban kamfanin samar da kayan aikin gona na jihar (KASCO), bisa zargin shi da sayar da hatsi mallakar gwamnati. 

Sanarwar da babban sakataren yaɗa labarai ga gwamnan Kano, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar, na cewa a ranar Talata 12 ga watan Satumban 2023 ne, Gwamna Abba Kabir, ya bayar da wannan umarni. 

Sanarwar ta ce ana zargin Dr. Tukur Ɗayyabu Minjibir, ne da sayar da hatsin gwamnati, ba ta hanyar da ta dace ba. 

Gwamnatin jihar ta umarci Dr Tukur Ɗayyabu, ya miƙa ragamar gudanar da kamfanin ga jami’i mafi girman muƙami nan take, ya zuwa lokacin da za a ji sakamakon ƙarin bincike.

Categories: Labarai
Tags: kano state
twinsem2:
X

Headline

You can control the ways in which we improve and personalize your experience. Please choose whether you wish to allow the following:

Privacy Settings