Gwamnatin Jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya ta karɓe iko da hedikwatar jam’iyyar NNPP a Maiduguri, babban birnin jihar.
Hukumar raya birane ta jihar ce ta ƙwace iko da ginin wanda ke haɗe da wasu ofisoshinta.
Jaridar BBC ta Wallafa cewa Dan takarar gwamnan jam’iyyar a Borno, Dr Umaru Alkali, shi ne ya bayyana wa manema labarai cewa jami’an tsaro sun tsare ɗan takarar sanata na jam’iyyar, Attom Muhammad Maigira, bayan ya amsa gayyatarsu.
Cikin waani saƙo da Muhammad Maigira ya aike wa manema labarai ya zargi Gwamna Babagana Umara Zulum na jam’iyyar APC da muzguna wa siyasarsu, yana mai cewa daga ofishin ‘yan sandan yake magana.
Lamarin na faruwa ne yayin da ɗan takarar shugaban ƙasa na NNPP, Rabiu Musa Kwankwaso ke shirin zuwa jihar a ƙarshen wannan makon.
Umaru Alƙali ya ce ya zuwa lokacin haɗa wannan rahoton, an jibge ‘yan sanda a sakatariyar jam’iyyar da ke Abbaganaram da Gidan Maradara domin hana ‘yan jam’iyyar shiga ofisoshinsu.