Gwamnatin Najeriya ta yi ƙarin kuɗin lambar mota da lasisi da kashi 50 cikin 100 a faɗin ƙasar.
A cewar wata sanarwa da ta fitar, ƴan Najeriya a yanzu za su ke biya naira 18,750 a maimakon naira 12,500 da ake biya a baya a matsayin kuɗin lambar motar kansu da kuma ta haya.
Sannan lamba ta musamman da a baya ake biya naira 80,000 a yanzu ya koma naira 200,000.
Lambar babur kuma za ta koma naira 5,000 maimakon 3,000, yayinda yin lamba uku zai koma naira dubu 30 daga dubu 20. Da wannan sabon tsarin karin ya kasance kashi 50 cikin 100.
Sannan lambar da mutum ke zaba ta koma dubu 50 daga dubu 40, yayinda lambobin musamman na gwamnati ta kamo dubu 20 daga dubu 15.
Lasisin tuki na shekara uku ya koma dubu 10 daga dubu 6, ban da kuɗaɗen da banki ke caji, lasisin shekara 5 ya koma dubu 15 daga dubu 10, yayinda lasisin masu tuka babur na shekara uku ya koma dubu 5 daga dubu 3, lasisin shekara 5 ya koma dubu 8 daga dubu 5.
An yanke wannan shawarar da bijiro da sabbin tsarin a taron da aka gudanar a Kaduna a ranar 25 ga watan Maris da masu ruwa da tsaki a wannan fani da kula da tittuna da tuki suka gudanar.