X

Gwamnati Ta Janye Shirin Kawar Da Tallafin Man Fetur-Abdulsalam Abubakar

Tsohon shugaban mulkin soja na Najeriya Janar Abdulsalam Abubakar ya bukaci gwamnatin Najeriya ta janye shirin kawar da dukan tallafin man fetur.

Janar Abdulsalami ya ce janye tallafin zai kara jefa talakawa ne a cikin karin kuncin tattalin arziki.

Tsohon shugaban mulkin sojan na magana ne a taron tattaunawa na jaridar Daily Trust na shekara, inda ya kasance shugaban taron.

Hakanan ya kara da jan hankalin gwamnatin cewa illar kalaubalen tsaro ta riga ta tsananta don haka janye tallafin zai kara tsananta lamura kawai.

Gwamnatin dai ta bakin shugaban kamfanin fetur NNPC Mele Kyari Kolo ta baiyana aniyar janye dukkan tallafin da hakan ka iya cilla litar man fetur daga Naira 320-340.

Categories: Labarai
twinsem2:
X

Headline

You can control the ways in which we improve and personalize your experience. Please choose whether you wish to allow the following:

Privacy Settings