Gwamnan Jihar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar shugabancin Najeriya a babban zaɓe na 2023 ƙarƙashin jam’iyyar adawa ta Peoples Democratic Party (PDP).
Tsohon Kakakin Majalisar Wakilai ta Najeriya, Tambuwal ya bayyana hakan ne a Sokoto babban birnin jihar a ranar Litinin bayan kammala tuntuɓa da neman shawara.
“Na saurari shugabannin jam’iyyarmu mata da matasa, game da kiran da suke yi na ya kamata na tsaya takara a ƙarƙashin babbar jam’iyyarmu ta PDP,” a cewarsa.
Ya ci gaba da cewa: “Lokacin da ‘yan Majalisar Wakilai ta 7 suka zo da buƙatarsu cewa na nemi kakakin majalisa, na ba su sharuɗa ciki har da cewa ina da magabata – marigayi Shehu Shagari, Aliyu Magatakarda Wamakko da wasu mutum biyu a Sokoto.
“Na faɗa musu cewa su je su tuntuɓi waɗannan shugabannin. Idan sun amince da buƙatarku zan yarda da ita kuma na nemi muƙamin.”
Ya zuwa yanzu, Tambuwal ne gwamna na biyu da ya bayyana sha’awarsa ta tsayawa takarar a PDP bayan Gwamnan Bauchi Bala Mohammed, yayin da Shugaba Buhari na APC zai gama wa’adi na biyu na mulkinsa a watan Mayun 2023.