X

Gwamnan Legas ya haramta acaɓa a jihar kwatakwata

Gwamnan Jihar Legas Babajide Sanwo-Olu ya haramta sana’ar acaɓa ko kuma okada kwatakwata a ƙananan hukumomi na jihar. 

A ranar Laraba ne gwamnan ya sanar da haramcin a ƙananan hukumomin cikin birni shida da kuma sauran ƙananan hukumomi tara masu tasowa na jihar. 

Ƙananan hukumomin da lamarin ya shafa su ne: Eti-Osa, Ikeja, Surulere, Lagos Island, Lagos Mainland, Apapa. Kazalika, haramcin ya shafi dukkan ƙananan hukumomin da ke ƙarƙashinsu. 

Gwamnan ya ba da umarnin ne ranar Laraba yayin wata ganawa da kwamashinan ‘yan sanda na jihar da sauran jami’an ‘yan sandan na yankuna. 

Ya ƙara da cewa nan da ranar 1 ga watan Yuni jami’an tsaro za su fara tabbatar da dokar kan masu baburan hayar. 

Matakin ya biyo bayan kashe wani makaɗi sakamakon taƙaddama a kan naira 100 cikin wata hatsaniya tsakaninsa da wasu ‘yan acaɓa, kamar yadda rahotanni suka bayyana. 

Da ma tun a shekarar 2020 gwamnatin jihar ta taƙaita ayyukan masu baburan.

Categories: Labarai
twinsem2:
X

Headline

You can control the ways in which we improve and personalize your experience. Please choose whether you wish to allow the following:

Privacy Settings