X

Gwamnan Kano Zai Naɗa Kwamishinoni Daga Dala, Fagge, Nassarawa

Gwamnan Kano,  Abba Kabir Yusuf ya miƙa wa Majalisar Dokokin jihar  takardar neman naɗa ƙarin kwamishinoni uku.

Kakakin Majalisar, Jibril Isma’il Falgore ne ya bayyana haka da safiyar Alhamis.

Ya ce mutanen da gwamnan ke neman naɗa wa un haɗa da Ibrahim Jibrin daga ƙaramar hukumar Fagge, Ibrahim Ali Namadi daga ƙaramar hukumar Dala, da Amina Abdullahi Sani daga ƙaramar hukumar Nassarawa.

Tun bayan da gwamnan ya miƙa sahun farko na jerin sunayen kwamishinoninsa ne ake samun ƙorafe-ƙorafe daga wasu ƙananan hukumomi da ba su samu wakilci a Majalisar Zartarwa ta jihar Kano ba.

Daga cikinsu akwai ƙananan hukumomin ƙwaryar birnin Kano da suka haɗa da Dala, Fagge, da Nassarawa.

Categories: Labarai
Tags: labarai
twinsem2:
X

Headline

You can control the ways in which we improve and personalize your experience. Please choose whether you wish to allow the following:

Privacy Settings