X

Gobara ta tashi a Kasuwar Singa a Kano

Wata gobara da ta tashi ta kone shaguna a wata shahararriyar kasuwar sayar da kayayyaki da ake kira Singer Market a jihar Kano. A cewar shaidun gani da ido Gobarar ta tashi ne da tsakar dare, amma…

Wata gobara da ta tashi ta kone shaguna a wata shahararriyar kasuwar sayar da kayayyaki da ake kira Singer Market a jihar Kano.

Gobarar, a cewar shaidun gani da ido, ta tashi ne da tsakar dare, amma ba a iya shawo kanta ba sai da misalin karfe 8 na safe.

Jami’an kashe gobara tare da ‘yan kasuwa sun yi kokarin shawo kan lamarin tare da kashe gobarar daga yaduwa zuwa wasu wurare.

Daya daga cikin ‘yan kasuwar, Abubakar Aminu, wanda shagonsa ya kone, ya ce da misalin karfe 1:15 na safe ne suka kira shi daga bakin gate, amma da ya isa kasuwar da misalin karfe 2:00 na safe, shagonsa ya kone, ya kasa kubutar da wani kaya.

A cewarsa, gobarar ta bazu zuwa wasu wuri guda uku da ke dauke da shaguna sama da 100 da aka ajiye da kayayyaki na miliyoyin naira.

“Gaskiya mun yi asara da yawa. Makwabcin da shi ma shagonsa ya kone kurmus ya ajiye tireloli uku na kaya a daren jiya. Yanzu duk sun kone,” inji shi.

Shi ma Basiru Dauda Kunya, ya ce gidan ana kiransa Gidan Sojoji kuma yana da shaguna kusan 10 a gaba da kuma shaguna a ciki. Gobarar ta kuma bazu zuwa gidan Savanah sannan ta nufi hanyar Bello Dandago.”

Categories: Labarai
Tags: MarketSinga
twinsem2:
X

Headline

You can control the ways in which we improve and personalize your experience. Please choose whether you wish to allow the following:

Privacy Settings