Wata gobara da ta tashi cikin dare ta kone wani bangare na kasuwar Gambarou, kasuwa ta biyu a cikin birnin Maiduguri, babban birnin jihar Borno.
Wannan na zuwa ne watanni biyar bayan wata gobarar dare makamanciyar ta ta kone wani bangare na kasuwar duniya a watan Maris din 2023.
Kawo yanzu dai ba a iya gano musabbabin tashin gobarar ba, amma jami’an kashe gobara na ci gaba da fafutukar kashe ta.
Wani ganau ya shaida wa wakilinmu ta wayar tarho cewa gobarar ta tashi ne daga shagunan sayar da kayan kamshi da hatsi na kasuwar.
Ya ce an baza jami’an tsaro a kasuwar domin kaucewa satar dukiya.