Hukumar kashe gobara ta jihar Kano ta ce gobara ta kone shaguna 37 a unguwar Zawaciki da ke karamar hukumar Kumbotso a jihar Kano.
Kakakin hukumar, Alhaji Saminu Abdullahi, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) cewa gobarar ta faru ne da misalin karfe 01:37 na safiyar Laraba.
A cewar Abdullahi, da misalin karfe 01:37 na safe ne wani Malam Baba ya kai mana waya cewa gobara ta tashi a Zuwaciki.
Mun yi gaggawar tattara jami’an mu zuwa wurin da abin ya faru da misalin karfe 01:47 na safe, muka kashe gobarar domin kada ta bazu zuwa wasu shaguna,” inji shi.
Abdullahi ya ce shagunan 37 sun kasance a kasan bene na wani gini mai amfani da yawa.
Ya kara da cewa wasu shaguna uku ne gobarar ta dan yi barna.
Ya ce ba a samu asarar rai ba, kuma ana binciken musabbabin tashin gobarar. (NAN)