X

Gobara Ta Kama Reshen GTBank A Abuja

Jaridar The PUNCH ta ruwaito cewa, wani reshe na bankin Guaranty Trust da ke yankin Mararaba a cikin babban birnin tarayya Abuja ya kone kurmus a safiyar ranar Juma’a.

Reshen GTBank yana kan hanyar Nyanya da Mararaba Expressway kafin titin Abacha, Karu. Mararaba gari ne mai iyaka, tsakanin FCT da Jihar Nasarawa.

Wani ma’abocin Twitter, @braunsyrup, da karfe 8:04 na safiyar ranar Juma’a, ya kira hankalin hukumar kashe gobara ta tarayya, da kuma GTBank kan lamarin gobarar.

Da aka tuntubi shugaban ayyuka na hukumar kashe gobara ta babban birnin tarayya Abuja, Amiola Adebayo, ya tabbatar da faruwar lamarin.

Ya ce, “Eh, gobara ta tashi a bankin, amma mun kashe ta.”

Wani rahoto da hukumar kashe gobara ta fitar ya ce gobarar wacce aka kashe da misalin karfe 8:40 na safe, ta faru ne sakamakon karfin wutar lantarki daga na’urar inverter.

Ya kara da cewa gobarar ta tashi ne daga dakin sabar da ke saman benen mai hawa daya.

Categories: Labarai
Tags: Gobara
twinsem2:
X

Headline

You can control the ways in which we improve and personalize your experience. Please choose whether you wish to allow the following:

Privacy Settings