Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano ta ce dakuna shida da suto biyu da dakunan girki biyu da bandakuna sun kome kurmus a gobarar.
Bayan samun nasarar kashe wutar, kakakin hukumar kashe gobara ta jihar Kano ta Saminu Yusif Abudullahi, ya ce wutar ta yi barna sosai a gidan.
Jami’in ya ce, “hukumarmu na gudanar da bincike domin gano musabbabin tashin goabarar, amma mazauna gidan sun alakanta ta da matsalar wutar lantarki.”
Ana zargin gobarar ta daren Lahadi ta fara tashi ne a daga dakin girki sannan ta bazu zuwa wasu sassan gidan, inda aka yi asarar dukiya mai tarin yawa