Zababben gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya yi zargin cewa gwamna Abdullahi Ganduje ya saki miliyoyin nairori ga shugabannin kananan hukumomin domin sake zaben ranar Asabar a jihar.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai ta hannun babban sakataren yada labarai na zababben gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa.
Ya ce, “Muna so mu sake ba da wata Shawarwari ga jama’a kan zargin yin amfani da kudaden gwamnati wajen gudanar da zabukan da za a kara a ranar Asabar 15 ga Afrilu, 2023.
“Muna da sahihin labari cewa Gwamnatin Jihar Kano karkashin jagorancin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ta bayar da umarnin sakin Naira miliyan 61 ga Doguwa, sama da Naira miliyan 60 ga Nasarawa, sama da Naira miliyan 60 ga Wudil. Haka kuma an jera wasu kananan hukumomin da za su karbi makudan miliyoyin Naira domin gudanar da zabuka.
“An saki kudin ne kawai don daukar nauyin ‘yan bangar siyasa don tada zaune tsaye a kan ‘yan kasa da mazauna jihar Kano da ba su ji ba ba su gani ba a lokacin zaben.
“Muna sake gargadin dukkan shugabannin kananan hukumomin da ma’aikatan gudanarwar su da suka hada da Daraktocin Ma’aikata (DPMs), Ma’aji, da sauran ma’aikata a matakin Jiha da Kananan Hukumomin da za su iya shiga kai tsaye ko a fakaice da wannan danyen aikin. al’amarin da ya shafi nisantar kansu da kuma tabbatar da cewa duk kudaden jama’a da aka fitar ba a yi amfani da su ba don irin wadannan dalilai kuma a mayar da su cikin asusun da ya dace.
“Yayin da muke yaba wa samari nagari da suka fito domin bayyana mana wasu munanan tsare-tsare da za a yi wa mutanen Kano gabanin zabe mai zuwa, ya dace a jawo hankalin daukacin ma’aikatan jihar cewa duk wanda aka samu yana so a kan wannan badakala zai fuskanci matakin da ya dace a lokacin da ya dace.
“Muna sane da cewa gwamnatin jihar ta shigo da dubban ‘yan daba daga ciki da wajen jihar Kano domin tada zaune tsaye. Don haka ya zama wajibi a yi kira ga jami’an tsaro da su gaggauta daukar mataki kan yiwuwar sake kai munanan hare-haren ‘yan daba a kan ‘yan jihar Kano da ba su ji ba ba su gani ba.”
Aminiya ta ruwaito cewa wannan na daya daga cikin jerin shawarwarin da gwamna mai jiran gado ya bayar tun bayan ayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben.
Gwamna Ganduje ya sha gaya masa cewa ya guji furta kalamai da ke kawo cikas ga gwamnati mai ci.