Hukumomi a Najeriya sun ce fursunoni 262 sun tsere daga gidan yarin Jos, babban birnin jihar Filato da ke arewacin kasar.
Wata sanarwa da hukumar kula da gyaran hali ta kasar ta fitar ranar Litinin ta ce fursunoni tara sun mutu yayin da ma’aikacin gidan yarin daya ya rasu, kana aka kashe dan bindiga daya yayin harin da wasu ‘yan bindiga suka kai a kurkukun ranar Lahadi da almuru.
Hukumomi sun ce maharan sun bude wuta sannan suka ci karfin masu gadin gidan yarin kafin su fasa inda fursunonin suke.
an sake kama fursunoni goma da suka tsere, yayin da har yanzu ake neman 252.
Babu tabbaci game da ainihin ‘yan bindigar da suka kai harin da kuma dalilinsu na yin hakan.
Tun da farko, hukumomin sun ce an ritsa da maharan a cikin gidan yarin, amma daga bisani sun ce sun tsere bayan kubutar da daruruwan fursunoni bayan kashe fursuna tara da ma’aikaci daya.
Gidan yarin yana kusa da hedikwatocin hukumomin tsaron kasar da ke birnin na Jos – wadanda suka hada da hedikwatar ‘yan sanda.
A baya bayan nan dai, hare-hare a gidajen yari a Najeriya sun ja hankalin ‘yan kasar.
Rahotanni sun nuna cewa an kubutar da fursunoni fiye da 800 a hare-haren da aka kai a gidajen yarin Kabba da ke jihar Kogi da Owerri da ke jihar Imo da kuma Oyo.