Majalisar zartaswa ta tarayya (FEC) ta amince da kudurin kasafin kudin shekarar 2024 da jimillar kashe naira tiriliyan 27.5.
Ministan Kasafin Kudi da Tsare Tattalin Arziki, Alhaji Atiku Bagudu ne ya sanar da hakan a ranar Litinin bayan taron majalisar ministocin tarayya da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya jagoranta a zauren majalisar da ke fadar shugaban kasa, Abuja.
Ministan ya kuma ce kudaden shigar da ake son samu a shekara mai zuwa ya kai Naira tiriliyan 18.
A cewarsa, za a fitar da karin bayani kan kasafin kudin a lokacin da shugaba Tinubu ya gabatar da kasafin ga majalisar dokokin kasar.
Bagudu ya kuma ce FEC ta kuma amince da sabon tsarin kashe kudi na 2024-2026 (MTEF)/ Fiscal Strategy Paper (FSP) wanda za a gabatar tare da kasafin kudin 2024
Majalisar zartaswa ta tarayya ta yi la’akari da kudurin kasafin kudin 2024. Tun da farko majalisar ta amince da MTEF. Yana da canjin N700 zuwa dala daya sannan kuma ma’aunin danyen mai ya kai $73.96 cents
“Don inganta kudaden shiga, majalisar ta kara yin nazari kan MTEF, inda aka samu canjin Naira 750 zuwa dala daya, da ma’aunin danyen mai ya kai dala 77.96. Hakan zai inganta kudaden shiga sosai,” inji shi.