X

Fasinjoji da dama sun mutu bayan da wani kwale-kwale ya kife a kogi

Fasinjoji da dama ne ake fargabar sun mutu bayan da wani kwale-kwale da ke jigilar ‘yan kasuwa ya kife a kogin Neja da ke Bagana a karamar hukumar Omala a jihar Kogi.

Dan uwan daya daga cikin mamacin mai suna Ibrahim Dantani wanda dan asalin Umaisha ne a karamar hukumar Toto ta jihar Nasarawa ya ce lamarin ya faru ne da misalin karfe 9:12 na daren Lahadi, inda kwalekwalen da ke dauke da fasinjoji sama da 47 ya kife.

Ya ce wadanda abin ya shafa wadanda yawancinsu ‘yan kasuwa ne kuma ’yan asalin garin Umaisha, suna komawa Umaisha ne bayan sun je wata kasuwa da ke garin Bagana.

An bayyana cewa, kwale-kwalen da ke cikin sauri ya yi karo da wata bishiya da ke tsakiyar kogin inda nan take ya kife.

“A gaskiya suna dawowa daga Bagana, kasuwar ƙauye ta kogin Niger suna komawa Umaisha lokacin da kwale-kwalen ya bugi wata bishiya a tsakiyar kogin kuma kwatsam ya kife,” in ji shi.

Ya ce an gano wasu gawarwaki, yayin da ake ci gaba da aikin ceto.

Ohimegye na masarautar Opanda-Umaisha, Mai Martaba Alhaji Usman Abdullahi, ya tabbatar da faruwar lamarin ta wayar tarho ga wakilinmu a ranar Litinin.

Ya ce wadanda abin ya shafa mutanen masarautarsa ne, da suka hada da wasu ’yan kasuwa Hausawa da ’yan fashi da ke dawowa daga kasuwar Bagana zuwa Umaisha.

“Har yanzu ban sami cikakkun bayanai da jimillar mutanen da suka yi hatsarin kwalekwale ba. Daya daga cikin mutanen fadara ne ya kira ni ya sanar da ni lamarin a lokacin da ba na nan,” inji shi.

Sarkin, duk da haka, ya ce zai dawo ga wakilinmu bayan ya isa gida don samun cikakkun bayanai kan wadanda suka mutu a lamarin.

Shi ma shugaban karamar hukumar Toto ta jihar Nasarawa Abdullahi Aliyu Tashas ya tabbatar da faruwar lamarin, sai dai ya ce har yanzu bai samu cikakken bayani ba.

Categories: Labarai
Tags: labarai
twinsem2:
X

Headline

You can control the ways in which we improve and personalize your experience. Please choose whether you wish to allow the following:

Privacy Settings