Gwamnan jihar Zamfara Bello Mohammed Matawalle ya yi kira ga Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da ya ayyana dokar ta baci kan sha’anin tsaro a fadin kasar.ABUJA, NIGERIA —
A yayin da yake marhabin da mataimakin babban sufeto Janar na ‘yan sandan Najeriya mai kula da shiyya ta 10, da ta kumshi jihohin Sokoto, Kebbi da Zamfara, Ali Janga, gwamnan jihar Zamfara Bello Matawalle, ya ce kafa dokar ta baci ne kadai mafita ga kalubalen tsaro da kasar ke fuskanta.
Matawalle ya bayyana cewa matsalar rashin tsaro ta kai wani mummunan yanayi da har tana kokarin fin karfin hukumomin tsaro, wanda hakan ya sa dokar ta baci ne kadai za ta iya kawo karshen matsalar.
Gwamnan ya ce jihar Zamfara ta fi kowace jiha dadewa tana fama da matsalar ‘yan bindiga masu kai hare-hare da kisan jama’a barkatai, da kuma satar mutane domin karbar kudin fansa.
“Matsalar tsaro a jihar Zamfara ta bambanta da dukkan sauran wurare, kuma tana bukatar ingantaccen Nazari da kwararan matakai domin kawar da ita” in ji Matawalle.
Jihar ta Zamfara dai na daga cikin jihohin da suka dade suna fama da matsalar ‘yan ta da kayar baya, wadda yanzu suke ci gaba da cin karensu ba babbaka, duk kuwa da kokarin da hukumomi suke cewa suna yi wajen yaki da wannan matsala.
Kiran na gwamnan na zuwa ne a daidai lokacin da aka ba da rahoton cewa ‘yan bindiga sun aike da wata wasikar barazana ga kwalejin ilimin fasahar kere-kere ta gwamnatin tarayya da ke Gusau, babban birnin jihar ta Zamfara.
Shugaban kwalejin Dr. Umar Bello ya tabbatar da samun wasikar wadda ya ce tuni ma da ta karade shafukan sada zumunta na yanar gizo.
To sai dai ya ce tuni da hukumar makarantar ta sanar da jami’an tsaro, kuma ana daukar matakan kare rayukan dalibai da ma’aikatan kwalejin.