Wani jigon jam’iyyar PDP a karamar hukumar Maiyama ta jihar Kebbi, Alhaji Abubakar Kurun-Kuku, tare da dimbin magoya bayansa sun sauya sheka zuwa jam’iyyar APC mai mulki.
Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya NAN ya ruwaito cewa an samu tarbar wadanda suka sauya sheka ne a wani gangamin da aka gudanar a garin Maiyama a ranar Talatar da ta gabata tare da dimbin jama’a da mambobin jam’iyyar APC karkashin jagorancin shugaban jihar Alhaji Muhammad Kana-Zuru.
Da yake sanar da sauya shekarsa tare da wadanda suka sauya sheka, Alhaji Abubakar Kurun- Kuku, ya ce halayen jagoranci na Gwamna Atiku Bagudu da yadda ya tafiyar da jihar a lokacin annobar cutar covid-19 ta sa suka koma APC.
“Mun koma APC ne saboda mun yi imani da kyakkyawan shugabanci na gwamnanmu, ci gaban da muka gani a jihar da kuma yadda ya iya sarrafa tattalin arzikin jihar a lokacin bala’in,” inji shi.
Har ila yau, mataimakin dan takarar gwamna na jam’iyyar APC, Sen. Umar Tafida, ya yaba da matakin da suka dauka na komawa jam’iyyar APC saboda ci gaban da aka samu a matakai daban-daban na kananan hukumomi, jihohi da tarayya.
Shugaban jam’iyyar APC na karamar hukumar Maiyama, Alhaji Sa’idu Giwa-Tazo, ya ba su tabbacin samun kyakkyawar kulawa a matsayinsu na ‘yan uwa na jam’iyyar APC a yankin.
Ya bayyana jin dadinsa yadda APC a Maiyama ta fi karfin a da.
Wasu daga cikin muhimman mutanen da suka halarci taron sun hada da mataimakin kakakin majalisar dokokin jihar Kebbi, Alhaji Usman Ankwai, kwamishinoni da masu bada shawara na musamman. (NAN).