X

“Dani aka sace yan makarantar Jangabe“ : inji Dan Fashin Daji

Wani ƙasurgumin ɗan bindiga mai satar mutane a Jihar Zamfara da ke arewa maso yammacin Najeriya ya ce matsalar rashin tsaro na ƙara ta’azzara ne a arewacin ƙasar saboda an mayar da lamarin na neman kuɗi.

Abu Sani wanda shi ne ya jagoranci sace ƴan matan sakandaren gwamnati ta garin Jengeɓe a bara, ya faɗi hakan ne a wani shiri na musamman na binciken ƙwaƙwaf da BBC ta gudanar kan ayyukan ƴan bindigar.

A jiya Litinin ne BBC ta saki shirin na Africa Eye a shafukanta na sada zumunta cikin Hausa da Turanci.

“An mayar da abin neman kuɗi a wannan ɓangare, kowa kuɗi yake nema,shi ya sa harkoki suke lalacewa, tun daga manyan har zuwa ga ƙananan,” in ji ɗan bindigar.

“Su kuma jami’ai su ma gwamnati idan ana rikici ana tura mata da kuɗi, ka ga ta wannan ɓangaren suna samu ke nan.

“Mu ma ta nan duk da dai za a zubar da jini a yi rashe-rashe, amma kuma a yi ta yi haka nan.”

A cikin hirar ya kuma bayyana cewa sai da gwamnatin Jihar Zamfara ta ba su fansar naira miliyan 60 kafin su saki ƴan matan sakandaren Jageɓe da suka yi garkuwa da su.

Sai dai gwamnatin ta daɗe da musanta cewa ta bayar da kuɗi kafin a sako ƴan matan.

Categories: Labarai
twinsem2:
X

Headline

You can control the ways in which we improve and personalize your experience. Please choose whether you wish to allow the following:

Privacy Settings